Isa ga babban shafi

Ecuador ta casa Qatar mai masaukin baki a gasar cin kofin duniya

A ranar Lahadi ne aka fara gasar cin kofin duniya a kasar Qatar, a daidai lokacin da aka fara gudanar da wasan kwallon kafa na tsawon wata guda, bayan da aka shafe shekaru 12 ana tafka muhawara kan karbar bakuncin gasar.

Wannan ne dai karon farko da Qatar ta fara halartar gasar cin kofin duniya a tarihin kasar.
Wannan ne dai karon farko da Qatar ta fara halartar gasar cin kofin duniya a tarihin kasar. REUTERS - KIM HONG-JI
Talla

Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani na Qatar ya halarci babban filin wasa na Al Bayt da ke Al Khor mai tazarar kilomita 50 a wajen Doha, domin kallon wasan da kasar ta kara da Ecuador.

A wasan da aka fara ba kakkautawa a filin wasa mai kama da tanti na Bedouin, Enner Valenica na Ecuador ya zura kwallon a raga bayan mintuna uku amma an soke kwallon sakamakon satar gida.

Bayan mintuna 13 ne Ecuador ta kuma zura kwallon bayan da Valenciayta zurawa mai tsaron ragar Qatar Saad Alsheeb a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Valencia ya kara kwallo da ci 2-0 kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Filin wasan na Al Bayt na daya daga cikin jerin sabbin filayen wasa da aka gina domin gudanar da gasar, wanda aka kiyasta cewa Qatar ta kashe dala biliyan 200, wanda ya zama gasar cin kofin duniya mafi tsada a tarihi.

Tauraron K-pop na Koriya ta Kudu Jung Kook ya jagoranci bikin bude taron na mintuna 30 wanda tauraron Hollywood Morgan Freeman ya kasance shugaban taron.

Ghanim Al-Muftah, dan gwagwarmaya ga nakasassu a kasar Qatar, tare da Freeman sun yi wa mahalarta taron: "maraba".

- Shirye-shiryen gasar -

Masu shirya gasar cin kofin duniya na fatan fara wasan kwallon kafa zai kwantar da cece-kucen da ya mamaye shirye-shiryen gasar tun bayan da aka ayyana kasar Qatar a matsayin mai masaukin baki a zaben da FIFA ta kada a shekarar 2010.

Halin da Qatar ke jefa ma'aikata 'yan ci-rani da kuma batun kare hakkin bil'adama na yankin Gulf ne ya mamaye batutuwan da suka shafi tunkarar gasar.

A ranar Asabar, Infantino ya ci gaba da kai farmaki cikin kakkausar murya na sukar da aka yi a taron, yana mai cewa yawancin sukar da aka yiwa kasar babu adalci a ciki.

"Wannan suka – babu gaira ba sabar - munafunci ne kawai," in ji Infantino.

"Bana so in bayar da wani darasi na rayuwa, amma abin da ke faruwa a nan da kuma yadda aka fassara shi babban rashin adalci ne."

-Tun farko dai ana ganin cewa takaddama za ta barke a gasar-

Kasashen Turai da dama da ke halartar gasar, wadanda suka hada da Ingila, Jamus da Denmark, sun ce 'yan wasan su za su sanya riguna masu launin bakan gizo don nuna goyon baya ga masu akidar auren jinsi. Bugu da kari luwadi haramun ne a kasar ta Qatar.

Matakin dai ya sa hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA za ta dauki matakin ladabtarwa, inda ta bayyana shirin samar da nata kayan aikin da za ta iya baiwa kungiyoyi.

Infantino ya dage cewa za a yi maraba da duk masu ziyartar gasar cin kofin duniya ba tare da la'akari da yanayin akidar jinsi ba.

"Na yi magana game da wannan batu tare da mafi girman jagoranci," in ji shi. "Za mu iya tabbatar da cewa zan iya tabbatar da cewa kowa ya samu karbuwa a wannan kasa yadda ya kamata."

- Benzema-

Kasar Faransa mai rike da kambun gasar ta sake samun kalubale a safiyar Lahadi bayan da aka tabbatar da cewa dan wasan gaba kuma wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or Karim Benzema ba zai iya fafatawa a gasar ba. Rashin Benzema koma baya ne ga tawagar Faransa

Ita ma Belgium tana fama da nata kalubalen bayan da aka cire dan wasanta Romelu Lukaku daga cikin tawagar da za su buga wasanni biyu na farko, yayin da yake ci gaba da murmurewa daga raunin da ya samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.