Isa ga babban shafi

An yi wa Casillas kutse a shafinsa na Twitter

Tsohon mai tsaron ragar Spain Iker Casillas ya ce an yi wa shafinsa na Twitter kutse, inda aka wallafa sakon da yake bayyana kansa a matsayin mai ra’ayin auren jinsi guda ko kuma dan daudu.

Iker Casillas.
Iker Casillas. AFP/Archivos
Talla

Cikin sakon, Casillas mai shekaru 41, wanda ya buga wa Real Madrid wasanni 725, kuma ya lashe gasar cin kofin duniya tare da Spain a shekarar 2010, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, yana fatan za’a girmama shi, domin shi din dan luwadi ne.

Sai dai, daga baya Casillas ya sake wallafa wani sakon a shafin nasa na Twitter, inda ya ce kutse aka yi masa, kuma an yi nasarar magance matsalar.

Tsohon golan ya kuma nemi afuwar dukkanin mabiyansa da kuma ga daukacin masu ra’ayi ko goyon bayan auren jinsi guda.

Shi ma dai tsohon dan wasan Spain da kungiyar Barcelona Carles Puyol ya nemi afuwa a shafinsa na Twitter, biyo bayan nasa sakon da ya wallafa na amsa Casillas, inda ya ce lokaci ya yi da za su ba da labarinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.