Jadawalin gasar zakarun Turai: Halaand zai hadu da tsohuwar kungiyarsa
Liverpool da Rangers za su hadua matakin rukuni na gasar zakarun nahiyar Turai, a yayin da Manchester City za ta hadu Borussia Dortmund, kungiyar da suka dauko dan wasan gabansu, Erling Halaand.
Wallafawa ranar:
Zakarun gasar Firimiyar Scotland, Cetic suna rukuni daya da masu rike da kofin, Real Madrid, a yayin da AC Milan za su gwabza da Chelsea a cikin rukuni guda.
Eintracht Frankfurt, wadanda wannan ne karon farko da suka tsinci kansu a matakin rukuni na gasar zakarun Turai suna rukuni daya da Tottenham.
Bayern Munich, Barcelona da Inter Milan duk suna rukuni guda.
Ga dai yadda cikakken jadawalin yake:
Rukunin A: Ajax, Liverpool, Napoli, Rangers
Rukunin B: Porto, Atletico Madrid, Bayer Leverkusen, Club Bruges
Rukunin C: Bayern Munich, Barcelona, Inter Milan, Viktoria Plzen
Rukunin D: Eintracht Frankfurt, Tottenham, Sporting Lisbon, Marseille
Rukunin E: AC Milan, Chelsea, RB Salzburg, Dinamo Zagreb
Rukunin F: Real Madrid, RB Leipzig, Shakhtar Donetsk, Celtic
Rukunin G: Manchester City, Sevilla, Borussia Dortmund, FC Copenhagen
Rukunin H: Paris St-Germain, Juventus, Benfica, Maccabi Haifa
Za a yi wasannin ne a tsakanin ranakun 6 ga watan Satumba da 2 ga watan Nuwamba.
Za a yi wasan karshe na gasar zakarun nahiyar Turai na wannan kaka a filin wasa na Ataturk da ke birnin Istanbul na kasar TUrkiya a ranar 10 ga watan Yunin shekarar 2023.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu