Isa ga babban shafi
Wasanni

Jadawalin gasar zakarun Turai ya hada Ronaldo da Messi a matakin rukuni

Hukumar UEFA ta fitar da sabon jadawalin gasar cin kofin zakarun Turai da ya kunshi kungiyoyi 24 a rukunin takwas daga A zuwa H.

Ana ganin rukunin G zai fi daukar hankali la'akari da yadda Messi da Ronaldo za su hadu.
Ana ganin rukunin G zai fi daukar hankali la'akari da yadda Messi da Ronaldo za su hadu. REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Jadawalin na UEFA ya nuna cewa Rukunin A na dauke da zakarar gasar ta bara: Bayern Munich da Atletico Madrid da Lokomotiv Moscow da kuma Salzburg wadanda za su kara tare da fitar da zakaru 2 da za su tsallaka zagayen kungiyoyi 16.

Rukunin B kuwa kamar yadda jadawalin ya nuna na dauke da: Real Madrid kana Shaktar Donetsk da Inter Milan sannan Borussia Monchengladbach.

Sai rukunin C da ya kunshi: Porto da Manchester City da Olympiakos da Marseille.

Rukunin D ya kunshi: Liverpool da Ajax sannan Atalanta da Midtjylland.

Rukunin E: akwai Sevilla da Chelsea da FK Krasnador da kuma Rennes.

Rukunin F: ya hada da Zenit St Petersburg da Borussia Dortmund da Lazio da kuma Bruges.

Rukinin G wanda ake ganin zai fi daukar hankali ya hadar da: Juventus da Barcelona da Dynamo Kyiv da kuma Ferencvaros, a dai wannan rukunin za a hadu da Ronald da Messi yayinda shi ma Suarez zai tunkari tsohuwar kungiyar ta sa Barcelona bayan sauya sheka a wannan kaka.

Rukunin H kuma na karshe ya kunshi: PSG da Manchester United sai RP Leipzig da Istanbul Basaksehir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.