Isa ga babban shafi
Wasanni

UEFA ta baiwa kungiyoyi damar canjin 'yan wasa 5 a gasar Zakarun Turai

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, ta yi shelar amincewa da soma aikin dokar baiwa kungiyoyin kwallon kafa damar kara adadin ‘yan wasan da suke sauyawa yayin fafata wasanni daga 3 zuwa 5.

Harabar hedikwatar hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA a birnin Nyon da ke kasar Switzerland.
Harabar hedikwatar hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA a birnin Nyon da ke kasar Switzerland. REUTERS/Denis Balibouse/File Photo
Talla

Matakin na UEFA ya biyo bayan kamala taronta a birnin Budapest na Hungray da ta yi a jiya Alhamis kan kudurin dokar.

UEFA ta ce dokar za ta soma aiki a gasar cin kofin zakarun Turai ta Champions League da kuma Europa a bana.

Zalika za a yi amfani da dokar kara adadin canjin ‘yan wasan a ragowar wasannin sabuwar gasar Nations League, da kuma wasannin neman cancantar halartar gasar cin kofin kasashen Turai.

Sai dai hukumar ta UEFA ba ta sanya gasar cin kofin kasashen Turan ta bana da coronavirus ta tilasta dagewa ba, cikin wadanda za su amfana da sauyin.

Masu horaswa da dama sun dade suna kiraye-kirayen kara adadin ‘yan wasan da suke da damar sauyawa a kowane wasa guda, domin rage gajiyar da ke addabar kungiya, musamman wadanda ke fafatawa wasanni masu yawa a ciki da wajen kasashensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.