Isa ga babban shafi
Wasanni

Tarihi zai maimaita kansa a sabon jadawalin gasar zakarun Turai

Hukumar kwallon kafar Turai UEFA ta fitar da jadawalin rukunin kungiyoyi 8 da suka rage a gasar cin kofin Nahiyar wadanda suka kunshi na Ingila 3 da na Jamus 2 dai dai daga Faransa Portugal da Spain.

Tambarin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League dake gudana a karkashin hukumar UEFA.
Tambarin gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League dake gudana a karkashin hukumar UEFA. AP - Claude Paris
Talla

Sabon jadawalin na UEFA ya nuna cewa zakarar Duniya mai rike da kambun Bayern Munich za ta hadu da PSG ta Faransa, wanda ke nuna tarihi zai maimaita kansa game da yadda kungiyoyin biyu suka hadu a wasan karshe na bara wanda kungiyar ta Faransa ta sha kaye.

A bangare guda wani tarihin zai sake maimaita kansa a haduwar Liverpool da Real Madrid kungiyoyin da suma suka hadu a wasan karshe na gasar a 2018.

Sai kuma haduwar FC Porto da Chelsea wanda ake ganin zai ja hankali matuka musamman la’akari da yadda Porto ta bayar da mamaki wajen fitar da Juventus daga gasar.

Jadawalin na uefa ya nuna hadda za a kuma kara tsakanin tawagar Pep Guardiola wato Manchester City da kuma Borussia Dortmund wadda ke ci gaba da nuna bajinta a wasannin gasar.

Dukkanin wasannin 4 za su gudana a ranakun 6 da 7 na watan Aprilu sai kuma haduwa ta biyu a ranakun 13 da 14 ga watan gabanin ficewar kungiyoyi 4 kana 4 kuma suci gaba a wasan gaba da na karshe.

Sanarwar UEFA ta nuna cewa wasan gab da na karshe na gasar za su gudana a ranakun 27 da 28 ga watan na Aprilu sai kuma zagaye na 2 a ranakun 4 da 5 ga watan Mayu, yayinda za a Karkare wasan karshe a ranar 29 ga watan a filin was ana Ataturk Olympic da ke Istanbul.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.