Isa ga babban shafi
Wasanni

Messi ya bi sahun Ronaldo wajen ficewa daga gasar cin kofin zakarun Turai

Lionel Messi na Barcelona ya bi sahun takwaransa Cristiano Ronaldo na Juventus wajen ficewa daga gasar cin kofin zakarun Turai, bayan canjaras dinsu a wasansu da PSG daren jiya Laraba.

Zakarun Duniya Cristiano Ronaldo na Juventus da Lionel Messi na Barcelona bayan ficewa daga gasar cin kofin zakarun Turai.
Zakarun Duniya Cristiano Ronaldo na Juventus da Lionel Messi na Barcelona bayan ficewa daga gasar cin kofin zakarun Turai. © Gonzalo Fuentes/Reuters et Luca Bruno/AP - Montage RFI
Talla

An dai ta shi wasan Barcelona na da 1 PSG na da 1 bayan soke kwallon Messi guda da ya zura a bugun fenariti, wanda ya bai wa PSG damar  rinjaye la’akari da cewa tun a haduwar farko ma kwallaye 4 ta zurawa Barcelonar.

A jumulla dai PSG ta zurawa Barcelonar kwallaye 5 yayinda ita kuma ta zura mata 2 a dukka haduwar.

Sai dai mai horar da kungiyar ta Barcelona Ronald Koeman ya ce Messi na da cikakkiyar masaniya kan makoma mai kyau da club din ke da shi a nan gaba duk da ficewa daga gasar ta cin kofin zakarun Turai a rukunin kungiyoyi 16.

Messi wanda ya dage kofunan gasar har sau 4 da Barcelona akwai jita-jitar da ke alakanta shi da komawa PSG da taka leda musamman bayan rashin katabus din kungiyar a wasannin bara.

Sai dai Koeman ya ce ficewarsu daga gasar a bana tafi kima idan aka kwatanta da ficewarsu a bara bayan shan kwallaye 8 daga hannun Bayern Munich mai rike da kambun gasar a yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.