Isa ga babban shafi

Za a yi wa ma’aikatan lafiya takwas shari’a kan mutuwar Maradona

Jami’an lafiya 8 za su gurfana a gaban kuliya bisa zarginsu da yin sakaci da lafiyar fitaccen dan wasan kwallon kafar Argentina, Diego Maradona, lamarin da ya kai ga mutuwarsa.

Fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Argentina, marigayi Diego Maradona.
Fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Argentina, marigayi Diego Maradona. AFP - -
Talla

Kawo yanzu dai ba a sanya ranar da za a fara shari’ar mutanen takwas ba, kan mutuwar Maradona a shekarar 2020, wadda masu gabatar da kara suka ce ta auku biyo bayan sakacin masu kula da lafiyarsa a lokacin da ake jinya a gida.

Maradona ya mutu yana da shekaru 60, a 2020 yayin da yake murmurewa daga tiyatar da aka yi masa a kwakwalwa saboda daskarewar jini, bayan da ya shafe shekaru da dama yana fama da matsalar shan tabar wiwi da barasa fiye da kima.

Wadanda suke fuskantar tuhumar hannu a mutuwar marigayi Maradona, sun hada da likitan kwakwalwa, wanda kuma yake kula da lafiyar iyalin tsohon dan wasan Leopoldo Luque, sai likitan kwakwalwa Agustina Cosachov, da masanin ilimin halayyar dan adam Carlos Diaz, da mai kula da lafiya Nancy Forlini, da kuma wasu mutane hudu ciki har da ma’aikatan jinya.

Masu gabatar da kara sun nemi da a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin kisan gilla.

Wadanda ake tuhumar suna fuskantar hukuncin daurin shekaru takwas zuwa 25 a gidan yari, muddin aka same su da laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.