Isa ga babban shafi

An sayar da rigar Maradona kan dala miliyan 9

Rigar da shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina, Diego Maradona ya saka a lokacin da ya zura kwallo biyu a ragar Ingila a wasan karshe na gasar cin kofin duniya a shekarar 1986, ciki har da wadda yayi amfani da hannunsa wajen jefa ta, an yi gwanjon sayar da ita kan dala miliyan 9 da dubu 300.

Rigar da Diego Maradona ya sanya yayin wasan karshe na gasar cin kofin duniya da Argentina ta doke Ingila da 2-1 a shekarar 1986.
Rigar da Diego Maradona ya sanya yayin wasan karshe na gasar cin kofin duniya da Argentina ta doke Ingila da 2-1 a shekarar 1986. AP - Jon Super
Talla

Kamfanin Sotheby da ya shara wajen kasuwancin sayar da zane-zane, da kayan ado, da kuma kayan tarihi da ke da hedikwata a birnin New York ne ya jagoranci gwanjon sayar da rigar ta Maradona.

'Yan kasuwa bakwai ne dai suka yi takarar sayen rigar ta Maradona, wadda aka fara gwanjonta daga ranar 20 ga watan Afrilu zuwa safiyar jiya Laraba 4 ga watan Mayu.

Kafin sayar da ita, rigar ta kasance mallakin dan wasan tsakiya na Ingila Steve Hodge, wanda ya musanya rigarsa da Maradona bayan da suka yi rashin nasara da 2-1 a birnin Mexico City, a wasan karshe na gasar cin kofin duniya.

Diyar Maradona dai ta so haifar da shakku kan cinikin a lokacin da ta yi ikirarin cewa rigar da aka yi gwanjon ita ce wadda mahaifinta ya saka a zangon farko na karawar wasan karshen da yayi da Ingila, ba wadda ya sanya a zagaye na biyu da ya ci kwallaye biyu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.