An yi tayin sayen rigar Maradona kan dalar Amurka miliyan 5
An fara gwanjon rigar da Diego Maradona ya sanya a lokacin da ya zura kwallaye biyu a ragar Ingila, cikinsu har da wadda yayi amfani da hannu wajen zura ta, a yayin gasar kofin duniya ta shekarar 1986.
Wallafawa ranar:
Bayanai dai sun ce tuni ma har an taya sayen rigar ta Maradona mai lamba 10 kan dalar Amurka sama da miliyan 5.
Za a cigaba da wannan gwanjo har zuwa ranar 4 ga watan Mayu mai zuwa.
Rigar dai a yanzu mallakin tsohon dan wasan tsakiya ce na Ingila Steve Hodge, wanda ya yi musayar ta da Maradona bayan da Argentina ta doke su da ci 2-1.
A kimanin shekaru biyu da suka gabata, bayan mutuwar Maradona a 2020, Hodge ya ce rigar gwarzon dan wasan ba ta siyarwa ba ce.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu