Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Vlahovic ya ci kwallo cikin dakika 32 a gasar Zakarun Turai

Dan wasan gaban a Juventus Dusan Vlahovic ya kafa tarihin zama mafi kankantar shekaru na biyu da ya ci wa kungiyar da ke Seria A kwallo a wasan farko da ya buga mata a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Dusan Vlahovic
Dusan Vlahovic © AFP
Talla

Allesandro Del Peiro ne kawai ya sha gaban Vlahovic wajen kafa irin wannan tarihi, domin kuwa ya ci wa Juventus kwallo a wasansa na farko ne cikin gasar Zakarun Turai yana da shekaru 20 daidai.

A daren jiya Talata ne dai, ya jefa kwallo a ragar Villareal bayan dakika 32 kacal da fara karawarsu, kwallon da ta zama mafi sauri da wani bako a gasar zakarun Turai ya ci.

Dan wasan da Juventus ta kulla yarjejeniya da shi daga Fiorentina bayan biyan Yuro miliyan 70, ya yi wannan bajintar ne, yana da shekaru 22 da kwanaki 25.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.