Isa ga babban shafi
Wasanni

United ta fice daga gasar Carabao, Chelsea ta tsallake rijiya da baya

Manchester United ta fice daga gasar cin kofin Carabao bayan da West Ham ta yi tattaki har filin wasa na Old Trafford ta kuma doke ta da 1-0, yayin fafatawar da suka yi a daren ranar Laraba.

Wasan gaba na Manchester United Anthony Martial, bayan ficewar su daga gasar cin kofin Carabao, inda West Ham ta doke su da 1-0.
Wasan gaba na Manchester United Anthony Martial, bayan ficewar su daga gasar cin kofin Carabao, inda West Ham ta doke su da 1-0. © CGTN
Talla

Nasarar da West Ham ta samu dai na a matsayin ramuwar gayya kan kayen da ta sha da kwallaye 2-1 a hannun Manchester United din a makon da ya gabata, yayin fafatawar da suka yi a gasar Firimiyar Ingila.

Zalika wasan kofin na Carabao shi ne nasarar da West Ham ta samu kan United a filin wasa na Old Trafford a karon farko tun shekarar 2007.

A sauran wasannin da aka kara, Chelsea da Tottenham sun tsallake rijiya da bayan a matakan bugun fanareti, inda suka samu nasarar tsallakawa zagaye a gasar kofin na Caraboa.

A wasan da aka kara tsakanin Chelsea da Aston Villa an tashi 1-1, a bugun fanareti kuma Chelsea ta yi nasara da 4-3, yayin da Tottenham ta doke Wolves da 3-2 a bugun na daga kai sai mai tsaron gida, bayan da aka tashi 2-2 a wasan da suka fafata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.