Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal na nazarin maye gurbin Arteta da Conte

Hukumar gudanarwar kungiyar Arsenal ta soma nazarin kulla yarjejeniya da tsohon mai horas da Chelsea da Inter Milan Antonio Conte domin maye gurbin kocinta na yanzu Mikel Arteta.

Antonio Conte tsohon mai horas da kungiyoyin Inter Milan, da Chelsea.
Antonio Conte tsohon mai horas da kungiyoyin Inter Milan, da Chelsea. MIGUEL MEDINA AFP
Talla

Kawo yanzu mai horas da Arteta ya rasa wasanni 20 cikin 60 da ya jagoranta, abinda ya sanya matsin lambar neman korarsa ke karuwa akan Arsenal, musamman bayan rasa wasanni biyu jere da juna a farkon kakar wasa ta bana, da suka hada da rashin nasara a wasan ta da Brentford da 2-0, sai kuma Chelsea da ta lallasa ta har gida da wasu kwallayen 2-0.

Kocin Arsenal Mikel Arteta.
Kocin Arsenal Mikel Arteta. Adrian DENNIS AFP/File

A baya bayan nan Jaridar UK Telegraph ta ruwaito cewa yanzu haka wasanni 5 kacal suka ragewa Arteta don ceton aikinsa na horas da Arsenal, kuma Antonio Conte tsohon kocin Inter Milan da Chelsea ke kan gaba tsakanin wadanda za su iya karbar jagorancin kungiyar ta Gunners.

A watannin baya ne dai aka rika alakanta Conte dan kasar Italiya da komawa gasar Firimiya don horas da kungiyar Tottenham Hotspur, amma yarjejeniyar ta gaza kulluwa.

Kididdiga ta nuna cewa Conte ya samu nasarar lashe wasanni 51 daga cikin 76 da ya jagoranci Chelsea a gasar Firimiya, zalika a karkashinsa ta lashe kofin kakar shekarar 2016 da 2017, kungiyar ta sallame shi a 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.