Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal na shan caccaka saboda rashin nasara sau 2 a farkon kakar wasa

To tun bayan wasannin karshen makon da suka gudana a gasar Firimiyar Ingila Arsenal ke shan caccaka daga magoya bayanta, masu sharhi, da kuma tsaffin ‘yan wasa ciki har da nata, sakamakon rashin nasarar da tayi da kwallaye 2-0 a hannun Chelsea.

Mai horas da kungiyar Arsenal Mikel Arteta.
Mai horas da kungiyar Arsenal Mikel Arteta. Adrian DENNIS AFP
Talla

Rashin nasarar ta ranar Lahadi dai itace ta biyu bayan kayen da Arsenal sha a wasanta da Brentford shi ma da kwallaye 2-0, abinda ya sanya a yanzu haka ta koma ajin ‘yan dagaji wato matsayi na 19 sakamakon rashin maki, makwanni 2 bayan fara sabuwar kakar wasan Firimiya.

Yayin da yake tsokaci kan halin da kungiyar ke ciki, tsohon dan wasan Arsenal Bacary Sagnia da ya buga mata wasanni 284, ya caccaki dukkanin masu ruwa da tsaki a shugabancin kungiyar inda yace muddin suka ci gaba da son rai da kuma nuna halin ko in kula dangane da sayen ‘yan awsan da suka dace, to fa ba s hakkah za su ci gaba shan kaye a wassanin da ke tafe.

A cewar Sagnia abin bakin ciki ne ganin yadda kimar tsohuwar kungiyarsa tasa ya zube duk da irin ficen da tayi a zamaninsu da kuma na wadanda suka gabace su.

Sai dai kocin Arsenal Mikel Arteta ko a jikinshi wai a tsikari kakkausa, domin kuwa yayin martini kan caccakar da ake musu cewa yayi, ko da wasa bai damu da bacin rai ko sukar kowa ba kan rashin nasarar da suka yi a wasansu da Chelsea.

A cewar mai horaswar abinda yake bukata shi ne ‘yan wasan da za su fuaknci kalubalen da ke gabansu tare da kawo karshensa.

A ranar 28 ga wannan watan Arsenal za ta kara da Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.