Isa ga babban shafi
Wasanni

Campbell ya yiwa Arsenal tayin maye gurbin Arteta

Tsohon dan wasan baya na Arsenal Sol Campbell ya yi kira ga shugabannin tsohuwar kungiyar ta sa da su bashi aikin horas da ita domin kawo karshen matsalolin da suka dabaibaiye ta a karkashin kocinta na yanzu Mikel Arteta.

Tsohon dan wasan Arsenal Sol Campbell yayin murnar zira kwallo a ragar FC Porto a gasar cin kofin zakarun Turai zagaye na 16 na filin wasan Dragon da ke birnin Porto, a Portugal. 17 ga watan Fabarairun 2010.
Tsohon dan wasan Arsenal Sol Campbell yayin murnar zira kwallo a ragar FC Porto a gasar cin kofin zakarun Turai zagaye na 16 na filin wasan Dragon da ke birnin Porto, a Portugal. 17 ga watan Fabarairun 2010. AP - Paulo Duarte
Talla

Rashin nasarar da Chelsea ta yi a gida da kwallaye 2-0 a Lahadin da ta gabata, na nufin Arsenal ta fara kakar gasar Firimiya Lig tare da rashin nasara guda biyu a jere, zalika ba bu ko da kwallo 1 da ta ci wasannin 2, karon farko a tarihin kungiyar.

Har ila yau, wannan shi ne karo na farko da Arsenal ke kasancewa a ajin karshe a teburin gasar ta Firimiya, tun bayan watan Agusta na shekarar 1992.

Campbell, wanda ya lashe gasar Firimiya sau biyu a lokacinsa tare da Arsenal gami da shahararriyar kakar da aka yiwa lakabi da ''Invincibles'' a turance ta 2003 zuwa 2004 ya ce akwai bacin rai a tattare da kallon wasannin Arsenal a halin yanzu.

Kawo yanzu mai horas da Arsenal Mikel Arteta ya rasa wasanni 20 cikin wasanni 60 da ya jagoranta, abinda ya sanya matsin lamba karuwa akan kocin.

A ranar Laraba Arsenal za ta kara da West Brom a wasan cin kofin Carabao, kafin su fafata da Manchester City mai rike da kambun gasar Firimiya a ranar Asabar.

Karin sakamako mara kyau dai zai sa Arteta shiga damuwa ya lura da yadda Arsenal kashe kudaden da yawansu ya kai Fam miliyan 130 wajen sayen ‘yan wasa a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.