Isa ga babban shafi
Wasanni

Ban yi nadamar kulla yarjejeniya da Arsenal ba - Ozil

Yayin da har yanzu ake dakon fayyace makomarsa a Arsenal, Mesut Ozil yace baya nadamar kulla yarjejeniya da kungiyar da kawo yanzu ya shafe akala shekaru 7 tare da ita.

Mesut Ozil
Mesut Ozil REUTERS/Hannah McKay
Talla

A shekarar 2013 Ozil ya sauya sheka da Real Madrid zuwa Arsenal kan fam miliyan 42 da rabi, inda kuma a tsawon lokacin da suke tare ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofunan FA 3, da na Community Shield 1, zalika ya lashe kyautar dan wasa mafi kwazo a kakar wasa ta 2015/2016.

Sai dai a baya bayan nan tauraron Ozil ya dusashe a kungiyar ta Arsenal, musamman bayan da Mikel Arteta ya karbi jagorancin horas da kungiyar, wanda ya cire Ozil daga tawagarsa baki daya a kakar wasa ta bana.

Sai dai duk wannan koma baya, Ozil yace bai taba yin nadamar kulla yarjejeniya da Arsenal ba.

Cikin wannan wata na Janairu ake sa ran dan wasan ya raba gari da kungiyar tasa, kuma Fanaberche dake kasar Turkiya ke kan gaba tsakanin kungiyoyin dake neman kulla yarjejeniya da Ozil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.