Isa ga babban shafi
Wasanni

United na nazari kan mutane 3 da ka iya maye gurbin Solksjear

Rahotanni daga Ingila na cewa shugabannin kungiyar Manchester United sun fara nazari kan mutane 3 da suka cancanci maye gurbin kocinsu na yanzu Ole Gunnar Solskjaer.

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer.
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer. Martin Meissner POOL/AFP
Talla

Solkjear dai na cikin matsin lamba sakamakon shan kashin da United ta yi da ci 2-1 a hannun Young Boys a gasar Zakarun Turai.

Magoya bayan United da kuma wasu masu sharhi kan kwallon kafa, sun caccaki matakin da Solskjaer ya dauka yayin wasan, inda ya maye gurbin Jadon Sancho da Diogo Dalot, bayan da aka kori Aaron Wan-Bissaka saboda jan kati.

Cristiano Ronaldo yayin karawar United da Young Boys a gasar Zakarun Turai.
Cristiano Ronaldo yayin karawar United da Young Boys a gasar Zakarun Turai. SEBASTIEN BOZON AFP

Sai kuma cire Cristiano Ronaldo da Bruno Fernandes da yayi, yayin da ya rage saura mintuna 20 a tashi, lokacin da wasa ke 1-1.

A halin yanzu United ta yi rashin nasara a wasanni 7 daga cikin 11 na gasar Zakarun Turai a karkashin Solskjaer, abinda ya sanya wasu fara kiraye -kirayen neman a sallame shi.

Tsaffin masu horas da kungiyoyin Inter Milan da Real Madrid, Antonio Conte da Zinaden Zidane yayin gaisawa da juna.
Tsaffin masu horas da kungiyoyin Inter Milan da Real Madrid, Antonio Conte da Zinaden Zidane yayin gaisawa da juna. © Libre Uso / Marca

Rahotanni kamar yadda jaridar UK Mirrow ta ruwaito na cewa, ana sa ran United ta tantance wanda za ta kulla yarjejeniya da shi, tsakanin Antonio Conte, Zinedine Zidane da Brendan Rodgers.

Conte da Zidane dai a yanzu haka babu wata kungiya da suke horaswa, bayan rabuwa da Inter Milan da Real Madrid, yayin da Rodgers ke jagorantar Leicester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.