Isa ga babban shafi
Wasanni

United ta sake mallaka wa Ronaldo lamba 7

Kungiyar Manchester United ta bada tabbacin cewa Cristiano Ronaldo zai sake sanya riga mai lamba 7 bayan komen da yayi mata, shekaru 12 bayan sauyin shekarar da yayi daga Kulob din a karon farko.

Cristiano Ronaldo yayin murnar jefa kwallo a ragar Newcastle a fafatawarsu ta gasar Firimiya cikin watan Fabarairu a. shekarar 2008.
Cristiano Ronaldo yayin murnar jefa kwallo a ragar Newcastle a fafatawarsu ta gasar Firimiya cikin watan Fabarairu a. shekarar 2008. ANDREW YATES AFP/Archives
Talla

Ronaldo mai shekaru 36 ne dai ya sanya rigar a lokacin da ya fara taka leda a kungiyar daga shekarar 2003 zuwa 2009, kafin ya koma Real Madrid, da kuma Juventus.

A waccan lokacin, Ronaldo ya ci wa United kwallaye 118 a wasanni 292 da ya buga mata, tare da taimaka mata wajen lashe kofuna tara, ciki har da na gasar Firimiya uku da na Zakarun Turai daya.

A baya bayan nan ne dai Angel Di Maria ya caccaki Manchester United kan yadda kungiyar ta ke baiwa riga mai lamba 7 matsayi na musamman.

Dan wasan na Argentina ya ce bai taba damuwa da gadon rigar mai lamba bakwai a Manchester United ba, a lokacin da ya koma kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.