Na kasa fahimtar dalilin United na fifita darajar riga mai lamba 7 - Di Maria
Angel Di Maria ya caccaki Manchester United inda yayi turr da yadda kungiyar ta ke baiwa riga mai lamba 7 matsayi na musamman.
Wallafawa ranar:
Dan wasan na Argentina ya ce bai taba damuwa da gadon rigar mai lamba bakwai a Manchester United ba, a lokacin da ya koma kungiyar.
Kawo yanzu dai fitattun ‘yan wasan da suka taka rawar gani da riga mai lamba 7 a Manchester United sun hada da Bryan Robson, Eric Cantona, David Beckham da Cristiano Ronaldo a shekarun baya.
Yanzu haka dai, komen da Ronaldo ya yi wa United shekaru 12 bayan rabuwarsu inda ya taka leda a Real Madrid da Juventus, kungiyar ta rubutawa mahukuntan gasar firimiya neman izinin Edinson Cavani ya canza lambar tawagarsa don baiwa Ronaldo damar sake saka rigar mai lamba 7.
Sai dai Di Maria da shima ya taka leda a Man United wanda kuma ya yi wasa tare da Ronaldo a Real Madrid, ya soki matakin inda ya ce ya kasa fahimtar mahimmancin da aka dorawa rigar mai lamba 7.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu