Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyoyin Firimiya sun hana bakin 'yan wasa zuwa kasashensu saboda Korona

Hukumar gasar Firimiyar Ingila ta sanar da cewa kungiyoyin ta ba za su kyale 'yan wasansu halartar wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da kasashensu za su buga ba a watan gobe.

Wasu 'yan wasan kungiyar Liverpool da suka hada da Roberto Firmino na Brazil, Sadio Mane na Senegal da kuma Muhammad Salah na kasar Masar.
Wasu 'yan wasan kungiyar Liverpool da suka hada da Roberto Firmino na Brazil, Sadio Mane na Senegal da kuma Muhammad Salah na kasar Masar. Laurence Griffiths POOL/AFP/File
Talla

Matakin dai ya shafi ‘yan wasan da kasashensu ke cikin wadanda Birtaniya ta bayyana a matsayin masu hatsari saboda fama da annobar Korona.

Jim kadan bayan sanarwar Firimiya ne kuma, gasar La Liga ta Spain ta ce za ta goyi bayan kungiyoyin da suka yanke shawarar kin sakin 'yan wasa zuwa kasashen da aka sanya cikin jerin masu hatsari saboda Korona, la’akari da cewa 'yan wasan da suka yi balaguro zuwa kasashen masu fama da cutar ta Korona, dole ne su bi ka'idojin kebe kansu bayan komawa Turai matakin da ka iya sanya ‘yan wasan rasa samun bugawa kungiyoyin nasu wasanni.

A halin yanzu wannan mataki na nufin kungiyoyi irinsu Liverpool ba za ta saki taurarinta da suka hada da Mohamed Salah ba, da Fabinho, Roberto Firmino da kuma Alisson Becker don wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na Brazil da kuma Masar.

'yan wasan Manchester City, Ederson da Gabriel Jesus.
'yan wasan Manchester City, Ederson da Gabriel Jesus. © Victoria Haydn/Man City via Getty Images

Kamar 'yan wasan Liverpool uku, taurarin Manchester City Ederson da Gabriel Jesus ma ba za su samu damar bugawa Brazil wasannin neman cancantar ba.

A takaice dai a Firimiya Lig kadai, kusan ‘yan wasa 60 ba za su samu damar zuwa kasashensu don haska musu a wasannin sharar fagen gasar cin kofin duniya da za su yi ba a wata mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.