Isa ga babban shafi
Wasanni - Gasar Zakarun Turai

Manchester United ta yi rashin nasara a hannun Young Boys

Tawagar kwallon kafa ta Young Boys ta yi nasarar lallasa Manchester United duk da kwallo guda da Cristiano Ronaldo ya zura mintuna 13 da fara wasa.

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Young Boys bayan nasarar lallasa Manchester United.
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Young Boys bayan nasarar lallasa Manchester United. SEBASTIEN BOZON AFP
Talla

Baiwa Aaron Wan-Bissaka jan kati ne ya fara ba United matsala duk da cewa ita ta ci gaba da jagoranci har zuwa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci inda Nicolas ya zurawa Young Boys kwallonta na farko a minti na 66.

Sauyin da Ole Gunnar Solskjear ya yi a minti na 95 ta hanyar cire Cristiano Ronaldo da Bruno Farnandes ya baiwa Young Boys damar zura kwallonta na biyu ta hannun Jordan Siebatcheu bayan kuskuren Jesse Lingard da ya maye gurbin Ronaldo.

Wasan na jiya shi ne irinsa na 177 da Ronaldo ya buga karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.

Bugu da kari kwallon Ronaldo mai shekaru 36 ita ce ta 3 da ya zurawa sabuwar kungiyar tasa tun baya kulla kwantiragi da ita a watan jiya.

Wasa na gaba da United za ta doka shi ne tsakanin ta da Villarreal ranar 29 ga watan nan.

A wasannin na jiya dai karkashin rukunin na F Villarreal ta yi canjaras ne da Atalanta da kwallaye 2 da 2 kungiyoyin da dukkaninsu ke dakon haduwarsu da United a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.