Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Ronaldo zai fara dokawa Manchester wasa a haduwarsu da Newscastle

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce haduwarsu da Newcastle United a gobe Asabar zai zamo wasa na farko da Cristiano Ronaldo zai taka leda biyo bayan dawowarsa tsohuwar kungiyar tasa.

Cristiano Ronaldo a wasan karshe da ya dokawa Manchester United.
Cristiano Ronaldo a wasan karshe da ya dokawa Manchester United. Andrew YATES AFP/File
Talla

Ronaldo dan Portugal mai shekaru 36 ya dawo tsohuwar kungiyar tasa ne a gab da lokacin kulle kasuwar musayar ‘yan wasan da ta gabata, lamarin da ya bayar da mamaki musamman bayan dogon rubutun dan wasan da ke nesanta kansa da raba gari da Juventus.

A shekarar 2009 ne dan wasan gaban na Portugal ya koma Real Madrid daga Manchester United gabanin barin Madrid zuwa Juventus.

Solskjaer ya bayyana cewa zai yi amfani da Ronaldo a wasan na gobe, sai dai bai yi karin bayani kan ko dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau 5 zai faro tun daga farko wasan ko kuma zai zo a sauyi ba.

Fiye da mako guda Ronaldo ya fara atisaye da ‘yan wasan Manchester United.

Bayan jerin ‘yan wasan da United ta saya ciki har da Jadon Sancho da Raphael Varane baya ga shi Ronaldo, babban aikin da ke gabanta shi ne kalubalantar takwararta Manchester City wajen lashe kofin Firimiya a cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.