Isa ga babban shafi
Wasanni

A karon farko cikin shekaru 20 Lazio ta kai zagayen gasar Zakarun Turai na 2

A karon farko cikin shekaru 20, kungiyar kwallon kafa ta Lazio ta samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen gasar zakarun Turai na biyu da ya kunshi kungiyoyi 16.

Dan wasan gaba na kungiyar Lazio Ciro Immobile yayin fafatawarsu da Club Brugge a gasar Zakarun Turai
Dan wasan gaba na kungiyar Lazio Ciro Immobile yayin fafatawarsu da Club Brugge a gasar Zakarun Turai Reuters
Talla

Lazio ta kai bantenta ne a jiya talata tashi 2-2 tsakaninta da Club Brugge, abinda ya bata damar kammala wasannin matakin rukuni na 6 da suke a matsayi na 2 da maki 10, biye da Borussia Dortmund mai maki 13.

Rabon da Lazio ta kai zagayen gasar zakarun turai na 2, tun kakar wasa ta tsakanin shekarun 1999 da 2000, lokacin da kungiyar ta kai zagayen kwata final na gasar ta zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.