Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasa da Messi babbar alfarma ce a gareni - Ronaldo

Tauraron kungiyar Juventus Cristiano Ronaldo ya ce alfarma ce babba a gare shi sake yin gasa tare da takwaransa na Barcelona Lionel Messi yayin wasan da suka fafata na jiya talata a gasar zakarun Turai na matakin rukuni.

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi yayin fafatawa tsakanin Juventus da Barcelona a wasan gasar zakarun Turai
Cristiano Ronaldo da Lionel Messi yayin fafatawa tsakanin Juventus da Barcelona a wasan gasar zakarun Turai Getty Images
Talla

Yayin fafatawar ta jiya Juventus da ta yi tattaki zuwa Spain ta doke Barcelona da kwallaye 3-0, kuma biyu daga ciki Ronaldo ne ya jefa daga bugun fanareti, yayin da Weston McKennie ya jefa 1.

Yayin tsokaci bayan wasan, Ronaldo ya ce bait aba kallo ko daukar alakarsa da Messi a matsayin hamayya ba, kamar yadda magoya bayansu ke ikirari.

Haduwar da aka yi tsakanin Ronaldo da Messi dai ita ce ta farko tun bayan da tauraron na Juventus ya rabu da gasar La Liga bayan sauyin sheka daga Real Madrid a gasar La Liga zuwa Seria A.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.