Isa ga babban shafi
Wasanni

Ya zama dole na cika burin sake zama kungiya daya da Messi - Neymar

Tauraron kungiyar PSG Neymar ya bayyana aniyar sake buga wasanni tare da Lionel Messi a kungiya guda.

Neymar, tauraron kungiyar PSG.
Neymar, tauraron kungiyar PSG. REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Neymar ya bayyana haka ne bayan nasarar da suka samu kan Manchester United a gasar zakarun Turai da kwallaye 3-1, wanda Neymar din ya ci biyu daga ciki.

Yayin zantawa da manema labarai Neymar ya ce ya zama dole a wannan karon burinsa na sake zama kungiya daya da Messi ya cika a kakar wasa mai zuwa.

A shekarar 2017 Neymar ya sauya sheka daga Barcelona zuwa PSG kan kudi mafi tsada a duniyar tamaula na Euro miliyan 222.

Kafin sauyin shekar Neymar da Messi da kuma Luis Suarez sun baiwa Barcelona gagarumar gudunmawa a nasarorin da samu na shekarun baya bayan nan, sakamakon kakkarfar hadin gwiwar masu zura kwallon da suka hada, bayaga nasibin iya sarrafa kwallon dalla dalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.