Isa ga babban shafi
Wasanni

Dillalin Pogba ya ce zaman dan wasan a United ya zo karshe

Dillalin tauraron Manchester United Paul Pogba, Mino Raiola ya yi shelar cewa zaman dan wasan a kungiyar ya zo karshe.

Paul Pogba, tauraron Manchester United
Paul Pogba, tauraron Manchester United Reuters/Jason Cairnduff
Talla

Sanarwar ba zatan na zuwa ne yayin da ya rage kasa da sa’o’i 24 Manchester United ta fafata da RB Leipzig a wasan karshe na matakin rukuni a gasar zakarun Turai.

An dai shafe watanni ana alakanta Pogba da sauyin sheka zuwa tsohuwar kungiyarsa ta Juventus ko kuma Real Madrid, wadda dan wasan da kansa ya sha bayyana burinsa na kulla yarjejeniya da ita.

A halin yanzu dai lokaci ne zai fayyace ko United za ta hakura da dan wasan nata mafi tsada da ta taba saye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.