Kungiyoyi 32 za su fara fafatawa a gasar cin kofin zakarun Turai
Yau Talata ne za a fara wasannin gasar cin kofin zakarun Turai, gasar da za a fafata tsakanin kungiyoyin kwallon kafar nahiyar ta Turai guda 32, wadanda aka kasa zuwa rukuni 8 dauke da kungiyoyi hur-hudu.
Wallafawa ranar:
Tun a jiya Litinin ne dai aka ga Lionel Messi na Barcelona ya koma filin atisaye bayan fama da jinya gabanin wasan na su na yau da za su kara da Borussia Dortmund a rukuin F.
Tun bayan wasanninsa na Copa America da Messin ya dokawa kasarsa Argentina cikin watan Yuli ba a sake ganin keyar Kaftin din na Barcelona a fili ba, inda ya rasa wasanni 4 na farkon wannan kaka, matakin da ya sanya Barcelonar rashin nasara a 2 daga cikin wasanninta 4 lokacin da baya nan.
To baya ga wasannin na Barcelona da Borussia Dortmund da kuma Inter Milan da Slavia Prague a rukunin F, akwai wasan Napoli da Liverpool baya ga Salzburg da KRC Genk a rukunin E.
A rukunin G akwai wasan Lyon da Zenit St Petersburg, kana wasan Benfica da RB Leipzig.
A rukunin H kuwa akwai wasan Ajax da Lille kana Chelsea da Valencia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu