Maurizio Sarri ya koma Juventus da horarwa
Maurizio Sarri ya raba gari da Chelsea domin karbar aikin horar da kungiyar kwallon kafa ta Juventus da ke buga gasar Serie A ta Italiya akan yarjejeniyar shekaru uku.
Wallafawa ranar:
Sarri wanda ya koma Chelsea daga Napoli a cikin watan Yulin 2018, ya jagoranci Chelsea wajen kammala gasar firimiyar Ingila ta bana a mataki na uku a teburi, yayinda ya kuma ya lashe mata kofin gasar Europa.
Yanzu haka, Sarri mai shekaru 60, zai maye gurbin Massimiliano Allegri wanda tuni ya bar Juventus a karshen kakar da ta gabata.
Rahotanni na cewa, kocin Derby County kuma tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea, wato Frank Lampard, shi ne zai maye gurbin Sarri a matsayin kocin Chelsea.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu