Isa ga babban shafi
Wasanni

Enyimba ta lashe gasar Premier ta Najeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Enyimba daga garin Aba, ta lashe kofin bana na gasar Premier ta Najeriya.

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Enyimba, bayan lashe kofin gasar Premier ta Najeriya a ranar laraba. 12/06/2019.
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Enyimba, bayan lashe kofin gasar Premier ta Najeriya a ranar laraba. 12/06/2019. ACLSports
Talla

Karo na takwas kenan da Enyimba ke lashe gasar ta Najeriya.

Kungiyar ta lashe kofin ne bayan nasarar da ta samu kan Akwa United da kwallaye 3-0 jiya laraba, a filin wasa na unguwar Agege da ke Legas, hakan ya bata damar kammala kwarya kwaryar gasar Super Six da ke zama karashen gasar Premier ta bana da maki 12, bayan buga wasanni 5.

An dai shirya gasar ta Super Six ce domin tantance zakarar gasar Premier ta Najeriya, da kuma wadanda za su wakilci kasar a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika CAF Champions League, da kuma CAF Confederations Cup, gasar cin kofin kalubalen nahiyar ta Afrika.

Kungiyoyi da suka kammala wasannin gasar Premier ta Najeriya a matakin na 1 zuwa na 3 ne a rukunin farko da na biyu suka fafata gasar ta Super Six.

Enyimba ce zakara da maki 12, sai Kano Pillars ta 2 da maki 11, bayan da itama a ranar larabar ta doke lobi stars da 1-0.

Enugu Rangers ke matsayi na 3 da maki 8, yayinda Akwa United ta kammala a matsayi na 4 da maki 6.

Lobi Stars ce ta 5 da maki 4, sai kuma ta karshe Ifeanyi Ubah da ta kammala wasannin na Super Six, karashen gasar Premier ta Najeriya babu maki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.