Isa ga babban shafi

Kofin nahiyar Afirka: Rohr ya soke suna Iheanacho

Babban kocin tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles, Gernot Rohr ya fitar da jerin sunayen ‘yan wasan da za su wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za fara ranar 21 ga watan Yunin nan da muke ciki, inda Kyaftin John Mikel Obi ke jagoranci.

Kyaftin tawagar Super Eagles ta Najeriya, Mikel Obi da Mai horarwa Gernot Rohr
Kyaftin tawagar Super Eagles ta Najeriya, Mikel Obi da Mai horarwa Gernot Rohr REUTERS/MATTHEW CHILDS
Talla

Mikel Obi, Ahmed Musa da Kenneth Omeruo dai ne ‘yan wasan da suka saura daga tawagar da ta lashe wa Najeriya kofin nahiyar Afirka a shekarar 2013 a Afirka Ta Kudu.

Najeriya wacce sau 3 tana lashe kofin nahiyar Afirka,ta gaza samun tikitin fafatawa a gasar har sau biyu, saboda haka, ‘yan wasa 20 da ke cikin wannan tawaga, zai kasance a karo na farko kenan da suke zuwa gasar.

Dan wasan gaba na Leicester City Kelechi Iheanacho da dan wasan tsakiya na Rotherham United Semi Ajayi sune ‘yan wasa biyu da Koch Gernot Rohr ya sauke daga cikin ‘yan wasa 25 da aka gayyata tun da farko.

Simon Moses na Levente da OLA Aina sun samu shiga tawagar bayan ba a dama da su ba a gasar cin kofin Duniya da ta gudana a Rasha 2018 saboda rauni.

Tawagar a Super Eagles ta bude sansasnin atisaye a garin Ismaila, kuma za tabuga wasan sada zumunta na karshe gabanin gasar ranar Lahadi mai zuwa.

A ranar 22 ga watan Yuni ne Najeriya za ta buga wasanta na farko a gasar da Burundi wacce ke gasar a karon farko.

Guinea da Madagascar ne sauran kasashen da Najeriya za ta gwada kwanjinta da su a matakin rukuni.

 

Ga sunayen ‘yan wasan Super Eagles din da zasu wakilci Najeriya da kungiyoyin da suke wasa :

 

Goalkeepers: Francis Uzoho (Anorthosis Famagusta/CYP), Ikechukwu Ezenwa (Katsina United), Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs/RSA)

Defenders: Olaoluwa Aina (Torino/ITA), Abdullahi Shehu (Bursaspor/TUR), Chidozie Awaziem (Caykur Rizespor/TUR), William Ekong (Udinese/ITA), Leon Balogun (Brighton & Hove Albion/ENG), Kenneth Omeruo (Leganes/ESP), Jamilu Collins (SC Paderborn 07/GER)

Midfielders: John Obi Mikel (Middlesbrough/ENG), Wilfred Ndidi (Leicester City/ENG), Oghenekaro Etebo (Stoke City/ENG), John Ogu (Hapoel Be'er Sheva/ISR)

Forwards: Ahmed Musa (Al Nasser/KSA), Victor Osimhen (Royal Charleroi/BEL), Moses Simon (Levante/ESP), Henry Onyekuru (Galatasaray/TUR), Odion Ighalo (Shanghai Shenhua/CHN), Alexander Iwobi (Arsenal/ENG), Samuel Kalu (Bordeaux/FRA), Paul Onuachu (FC Midtjyland/DEN), Samuel Chukwueze (Villarreal/ESP)

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.