Isa ga babban shafi
Wasanni

Har yanzu Super Eagles na bukatar Moses - Rohr

Mai horar da tawagar kwallon kafa Super Eagles ta Najeriya, Gernot Rohr, ya ce zai yi farin cikin ganin dan wasansa Victor Moses ya janye matakinsa na yin ritaya daga bugawa kasarsa kwallo.

Victor Moses yayin murnar jefa kwallo a ragar Argentina, yayin gasar cin kofin duniya ta 2018 a Rasha.
Victor Moses yayin murnar jefa kwallo a ragar Argentina, yayin gasar cin kofin duniya ta 2018 a Rasha. REUTERS/Toru Hanai/File Photo
Talla

Yayin da yake tsokaci kan matakin na Moses, Rohr ya ce Najeriya tana maraba da dawowarsa domin ci gaba da wakiltarta, musamman ma, idan dan wasan yana samun damar bugawa kungiyarsa a nahiyar turai wasanni sosai.

A shekarar 2018, Victor Moses ya sanar da yin ritaya daga bugawa Najeriya kwallo, yana da shekaru 27, kwanaki kadan, bayan kammala gasar cin kofin duniya da Rasha ta karbi bakunci, wadda Najeriya ta gaza fita daga matakin rukuni zuwa zagaye na gaba.

A waccan lokacin Moses ya ce ya yanke shawarar ce saboda ya samu damar lura da iyalansa, zalika zai mayar da hankali wajen karfafa kwazon wasannin da ya bugawa kungiyarsa ta Chelsea.

Sai dai ba kamar lokacin kakar wasa ta 2016/2017 ba yayin a zamanin horarwar Antonio Conte, bayan da sabon mai horarwa Maurizio Sarri ya karbi ragamar kungiyar Chelsea, wasanni kalilan kawai Moses ya samu bugawa, lamarin da ya tilasta mishi soma neman kungiyar da zai koma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.