Isa ga babban shafi
Wasanni-kwallon kafa

Manchester City da Liverpool na tseren lashe kofin Firimiya

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta sake komawa matsayin Jagora a teburin Firimiya, bayan nasara kan Burnley da kwallo 1 da nema, sai dai a wannan karon tazarar maki daya ne cal tsakaninta da Liverpool yayinda dukkaninsu ke da ragowar wasanni bibbiyu kafin karkare gasar.

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Reuters
Talla

Yayin wasan na jiya wanda ya gudana a gidan Burnley, Sergio Aguero ne ya yi nasarar zura kwallon daya tal a minti na 64 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Tun bayan wasan dab da na kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai da Tottenham ta lallasa City har yanzu bata kara rashin nasara a wasannin da take dokawa gida da waje ba.

Tazarar da ke tsakanin Liverpool da Mancity dai ita ce tazara mafi kurkusa da aka taba samu a Tarihin gasar Firimiya cikin shekarun baya-bayan nan, haka zalika idan har dukkaninsu suka yi nasara a wasanninsu bibbiyu da ya rage musu City za ta dage kofin da banbancin maki daya cal tsakaninta da Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.