Isa ga babban shafi
Wasanni-kwallon kafa

Liverpool ta koma gurbinta na Jagora a Firimiya

Liverpool ta koma matsayinta na jagora a teburin gasar bayan lallasa Cardiff City da kwallaye 2 da banza, inda yanzu ta ke da maki 88 tazarar maki 2 tsakaninta da Manchester City, ko da dai Cityn na da wasa guda a hannu.

Roberto Firmino da Naby Keita bayan nasararsu kan Cardiff City da kwallaye 2 da banza
Roberto Firmino da Naby Keita bayan nasararsu kan Cardiff City da kwallaye 2 da banza Action Images via Reuters/Carl Recine
Talla

Kwallayen biyu da Wijnaldun da kuma James Milner suka zura a ragar Cardiff din ne ya bai wa Liverpool damar komawa matsayinta, bayan da a ranar asabar City ta samu zarafin hayewa saman teburi sakamakon lallasa Tottenham.

A larabar makon nan ne dai Liverpool za ta fayyace idan za ta iya dage kofin a bana ko akasin haka, wato bayan wasan Manchester City da Manchester United.

Matukar dai City ta gaza lallasa United a wasan na ranar Laraba to da alama fa Liverpool za ta kawo karshen dakonta na tsawon shekaru 29 don lashe kofin na Firimiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.