Isa ga babban shafi
Wasanni

'Yan wasan United ba su mutunta Mourinho ba - Keane

Tsohon dan wasan Manchester United kuma kaftin dinta Roy Keane, ya ce bai ji dadin yadda wasu ‘yan wasan kungiyar suka rika nuna murna a fili ba, dangane da korar tsohon kocinsu Mourinho.

Tsohon dan wasan Manchester United Roy Keane.
Tsohon dan wasan Manchester United Roy Keane. Darren Staples / Reuters
Talla

Keane ya kuma soki yadda wasu daga cikin ‘yan wasan na United basu mutunta tsohon kocin na su yadda ya kamata ba yayin da suke tare.

Tsohon dan wasan na United, ya ce irin wannan halayya ta zama ruwan dare gama duniya a tsakanin ‘yan wasan kwallon kafa na yanzu, wadanda ya kira da masu tattare da wani nau’i na kasawa.

Yayin zamaninsa a United Roy Keane ya shafe shekaru 13 tare da kungiyar, inda ya taimaka mata wajen lashe kofunan gasar Premier 7, kofunan FA 4, da kuma kofin gasar zakarun Turai guda 1.

A ranar Talata Kungiyar Manchester United ta kori Jose Mourinho daga bakin aiki, saboda matsalolinta da ta ce ya gaza magancewa, inda ta maye gurbinsa da tsohon dan wasanta Ole Gunnar Solskjaer a matsayin mai horarwa na wucin gadi zuwa karshen kakar wasa ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.