Isa ga babban shafi
Wasanni

Giggs ya baiwa United shawara kan makomar Mourinho

Mai horar da tawagar kwallon yankin Wales na Birtaniya, kuma tsohon dan wasan Manchester United Ryan Giggs, ya shawarci kungiyar da ta kara hakuri da mai horar da 'yan wasanta Jose Mourinho kada ta kore shi.

Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho.
Mai horar da kungiyar Manchester United Jose Mourinho. Reuters/Robert Pratta
Talla

Giggs ya ce koda yake United na fuskantar kalubale a halin yanzu, yana da kwarin gwiwar lamarin zai sauya, kuma nasara zata sake ziyartar kungiyar.

Mourinho na fuskantar suka daga ciki da wajen kungiyar ta United, ganin yadda ya jagoranci wasanni hudu ba tare da samun nasara ba, a gefe guda kuma, ga rashin kyakkyawar alakar dake dada bayyana tsakaninsa da Paul Pogba, dan wasan kungiyar mafi tsada.

A baya bayan nan dai wasu daga cikin masu sharhi kan wasanni, na da ra'ayin zai yi wahala a ce kungiyar ta United bata sallami Mourinho, ida wasu ke zaton cewa mai yiwuwa tsohon mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ya maye gurbinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.