Salah zai iya lashe kyautar Ballon d'Or - Wright
Tsohon dan wasan gaba na kungiyar Arsenal Ian Wright, ya ce akwai yiwuwar Mohammed Salah ya samu nasarar lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Ballon d’Or ta bana.
Wallafawa ranar:
Wright ya ce Salah zai iya samun wannan nasara muddin ya jagoranci kungiyarsa ta Liverpool wajen lashe kofin gasar zakarun nahiyar turai.
Zuwa yanzu Salah dan kasar Masar, ya ci jimillar kwallaye 43 a wasanni 47 da ya bugawa Liverpool, tun bayan barin tsohuwar kungiyarsa ta Roma.
A cewar Ian Wright baa bun mamaki bane Mohammed Salah ya kawo karshen mamaye kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka yi tun daga shekarar 2008.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu