Na fi son lashe kofin zakarun Turai fiye da komai- Salah
Dan wasan gaba na Liverpool, Mohamed Salah ya ce, lashe kofin gasar zakarun Turai ya fi muhimmanci a gare shi fiye da duk wata kyauta da zai lashe shi kadai a kakar bana.
Wallafawa ranar:
Kawo yanzu dai, Salah, dan asalin Masar kuma mai shekaru 25, ya jefa kwallaye 40 a raga a cikin wannan kaka, yayin da kuma ya lashe kyautar gawarzon dan wasan firimiyar Ingila na wata-wata sau uku, kuma shi ne dan wasa na farko da ya lashe kyautar sau uku a kaka guda.
Salah ya lashe kyautar a cikin watannin Nuwamba da Fabairu da kuma Maris da suka gabata.
Sai dai dan wasan ya ce, daukan kofin zakarun Turai a bana, shi ne mafi muhimmanci a gare shi fiye da duk wata kyauta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu