Isa ga babban shafi
wasanni

Holland ta rasa gurbi a Rasha, Italiya na cikin barazana

Kaften din tawagar kwallon kafa ta Holland, Arjen Robben ya yi ritaya daga buga wa kasarsa tamaula bayan sun gaza samun gurbi a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a badi.

Arjen Robben ya yi ritaya bayan ya gaza samar wa Holland gurbi a gasar cin kofin duniya a Rasha
Arjen Robben ya yi ritaya bayan ya gaza samar wa Holland gurbi a gasar cin kofin duniya a Rasha REUTERS/Paulo Whitaker
Talla

Robben shi ne ya zura kwallaye biyu a fafatawar da suka yi da Sweden wacce ba ta zura ko guda ba, amma duk da haka yawan kwallayen ba su isa su bai wa Holland damar buga wani wasan neman gurbi ba.

Dan wasan mai shekaru 33 ya buga wa kasarsa wasanni 96, in da ya ci ma ta kwallaye 37.

Sannan kuma ya na cikin tawagar Holland da ta kammala a mataki na uku a gasar cin kofin duniya ta 2014 wadda Jamus ta lashe.

A bangare guda, yanzu haka Italiya wacce ta yi fice a fannin tamaula a duniya, na cikin kasashen Turai takwas da za su sake buga wasannin neman gurbi a gasar cin kofin duniyar.

Italiya dai ta lashe kofin duniya har sau hudu.

Sauran kasashen da za su sake buga wasan neman gurbin a Turai sun hada da Switzerland da Croatia da Denmark da Arewacin Ireland da Jamhuriyar Ireland da Girka da Sewden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.