Isa ga babban shafi
wasanni

Messi ya tsallakar da Argentina zuwa gasar kwallon duniya

Lionel Messi ya taimaka wa Argentina samun gurbi a gasar cin kofin duniya da za a gudanar a Rasha a badi bayan ya zura kwallaye uku a fafatawar da suka yi da Ecuador a jiya, yayin da Chile ta sha kashi a hannun Brazil da ci 3-0, abin da ya kara taimaka wa Argentina samun gurbin cikin sauki.

Linoel Messi na Argentina
Linoel Messi na Argentina Fuente: Reuters/Henry Romero
Talla

Yanzu haka Argentina na mataki na uku da maki 28 a teburin gasar neman gurbin a kudancin Amurka, in da Brazil da Uruguay ke a matsayi na daya da biyu.

Kwallaye ukun da Messi ya cilla a ragar Ecuador wadda ta zura daya, sun kawo karshen fargabar da ake yi na rashin tabbacin zuwan Argentina Rasha.

Yanzu haka dai, Messi zai halarci gasar cin kofin duniya a karo na hudu a tarihinsa na kwallon kafa, in da zai yi fatan kai kasarsa ga gaci.

Argentina dai ta lashe kofin duniya sau biyu, yayin da ta kai matakin wasan karshe a gasar ta kofin duniya a shekarar 2014 amma Jamus ta doke ta.

Shi ma Christiano Ronaldo na Portugal zai halarci Rasha bayan sun samu nasara akan Switzerland da ci 2-0.

Sai kuma Faransa da ta samu gurbi baya ta casa Belarus da ci 2-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.