Isa ga babban shafi
La liga

Barcelona ta tabbatar Neymar zai raba gari da ita

Barcelona ta tabbatar a yau Laraba cewa Neymar na son rabuwa ta ita, inda ta jaddadawa Paris Saint-Germain sai ta aje jimillar kudi yuro miliyan 222 kafin ta karbi dan wasan.

Neymar na Brazil
Neymar na Brazil LLUIS GENE / AFP
Talla

Barcelona ta fadi a cikin wata sanarwa a shafinta na intanet cewa Neymar tare da mahaifinsa sun sanar da ita bukatar dan wasan na barin kungiyar.

Barcelona kuma ta shaidawa Neymar cewa dole sai PSG ta biya jimillar kudi miliyan 222 na yuro, kuma ta amince ya kaucewa fitowa atisaye.

Neymar zai kasance dan wasa mafi tsada a duniya idan har PSG ta biya kudaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.