Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Neymar zai sake gurfana a Kotu

Dan wasan Barcelona Neymar na Brazil zai sake gurfana a gaban kotu akan badakalar zargin cogen cinikin shi daga Santos zuwa Barcelona bayan an yi watsi da karar a watan Yuli.

Neymar na Brazil da ke taka leda a Barcelona ta Spain
Neymar na Brazil da ke taka leda a Barcelona ta Spain REUTERS/Eloy Alonso
Talla

A 2013 ne Barcelona ta sayo Neymar daga Santos ta Brazil.
Amma a jiya aka sake bude karar da wani kamfani saka jari ya shigar da ke ikirarin an cuce shi kan cinikin Neymar zuwa Barcelona daga Santos.

Kamfanin na DIS ke da hakkin mallaka na Neymar, kuma yana zargin bai samu kudaden da ya kamata ace ya samu ba na cinikin dan wasan.

amma dan wasan da mahaifin shi da ake zargi da yin cogen dukkaninsu sun musanta cewa an yaudari kamfanin

Kamfanin dillacin labaran Spain ya ce Neymar da mahaifinshi da shugabannin kungiyar Barcelona ake zargi da badakalar cinikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.