Isa ga babban shafi
Wasanni

Valverde ya zama kocin Barcelona

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta tabbatar da tsohon kocin Athletico Bilbao, Ernesto Valverde a matsayin sabon mai horar da ita, in da ta kulla kwantiragin shekaru biyu da shi.

Ernesto Valverde, sabon kocin Barcelona
Ernesto Valverde, sabon kocin Barcelona REUTERS
Talla

Shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya ce, sabon kocin na da kwarewa da ilimin horar da ‘yan wasa.

A makon jiya ne Valverde da ya taba buga wa Barcelona wasa, ya sanar da shirinsa na raba gari da Atletico Bilbao bayan ya jagorance ta na tsawon shekaru hudu.

Valverde mai shekaru 53 zai maye gurbin Luis Enrique, wanda ya ce zai raba gari da Barcelona bayan kwantiraginsa na shekaru uku ya kare.

Tuni dai Barcelona ta yi sallama da Enrique bayan ya jagorance wajen samun nasarar lashe kofin Copa de Rey bayan ta casa Alaves da ci 3-1 a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.