Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Qatar ta gama ginin Filin kwallon kafa mai AC

Qatar ta sanar kammala aikin ginin daya daga cikin filayen wasannin kwallon kafa domin wasannin gasar cin kofin duniya da za ta karbi bakunci a 2022.

Filin kwallon kafa na Khalifa a Qatar
Filin kwallon kafa na Khalifa a Qatar REUTERS
Talla

An kamala ginin da fasahohi da za su samar da ni’ima ga ‘yan wasa da ‘yan kallo.

Akwai fasahar da aka samar da za ta dinga feso ruwan sanyi a filin, baya ga na’ura da za ta sanyaya filin wasan.

Tsohon filin wasa ne Qatar da gyara domin gasar cin kofin duniya a 2022.

Wannan na daya daga cikin kalubalen da Qatar ta fuskanta kafin samun damar daukar nauyin wasannin saboda matsanancin zafin da ake yi lokacin da aka saba gasar cin kofin duniya a watan Juni zuwa Yuli.

Za a bude katafaren filin da wani babban wasa a Qatar tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafar kasar wato Al Sadd inda tsohon dan wasan Barcelona Xavi Hernandez ne kaftin da kuma kungiyar Al Rayyan.

Filin na Khalifa zai dauki ‘yan kallo dubu 40 wanda shi ne na farko da aka kammala, kuma Qatar za ta yi amfani da bikin na gobe domin nunawa duniya cewa a shirye ta ke ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.