Falcao da Coentrao na fuskantar shari'a
Lauyoyi a kasar Spain sun shigar da kara kan zargin da suke yi wa ‘yan wasan kwallon kafa da suka taka leda a kasar guda biyu, Radamel Falcao da kuma Fabio Coentrao, na boyewa ma’aikatar tattara harajin kasar, ainahin albashin da suke karba tsakanin shekarun 2012 da 2014.
Wallafawa ranar:
Jimillar kudaden harajin da lauoyoyin da ake zargin ‘yan wasan da kin biya ya kai euro miliyan 7.
Ana zargin Falcao, wanda a baya ya bugawa kungiyar Atletico Madrid a Spain, amma yanzu yake Monaco ta Faransa, da kin bayyana akalla euro miliyan 5 da dubu 600 da ya dafe a zamanin da yake taka leda a gasar Laliga.
Shi kuwa Fabio Centrao da ke kungiyar Real Madrid yanzu haka, an zarge shi ne da boye euro miliyan 1 da dubu 300 da ya karba a matsayin albashi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu