Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo na gaf da kafa sabon tarihi

Dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo na gaf da kafa tarihi na zama dan wasan da yafi kowa zura kwallaye a lig mafi karfi guda biyar a nahiyar turai bayan nasarar da ya samu na kamo dan wasan Ingila da ke rike da tarihin Jimmy Greaves a lokacin da ya zura kwallaye biyu a wasan da Madrid tayi da Sevilla a ranar Lahadi.

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya, Cristiano Ronaldo, na kungiyar Real Madrid.
Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Duniya, Cristiano Ronaldo, na kungiyar Real Madrid. Reuters / Paul Hanna Livepic
Talla

Ronaldo ya kamo Greaves da ke da kwallaye 366, kuma ya hada wannan jimlar kwallaye ne lokacin zaman sa da Manchester United inda ya zura kwallaye 84, sai kuma Real Madrid da ya ke wasa a yanzu, da ya zura kwallaye 282.

Gerd Muller na kasar Jamus shi ne na biyu da kwallaye 365, sai kuma abokin hamayyarsa Lionel Messi na Barcelona shi ne na uku, wanda ya zura kwallaye 346 a cikin shekaru 13 da fara murza leda.

Yanzu dai ana jiran a gani ko Ronaldo zai kafa wannan tarihi nan da ranar Laraba, inda Real Madrid zata kece raini a wasan La liga da kungiyar Celta Vigo.

An dai dade ana jiran kwantan wasan domin sanin makomar gasar ta La liga, ganin cewa Barcelona da Real Madrid na tafiya kai da kai, kowanne da maki 87, sai dai banbancin yawan kwallaye ne ya raba su inda Barcelona keda yawan kwallaye 77 yayin da Real Madrid keda 60.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.