Isa ga babban shafi
Spain

Wasanni 40 ba a samu galabar Real Madrid ba

Real Madrid na ci gaba da samun galaba inda ta buga wasanni 40 ba a doke ta ba a kakar bana bayan ta sha da kyar a karawar da ta yi da Sevilla inda suka tashi ci 3-3 a gasar lashe kofin Sarkin Spain Copa del Ray.

Real Madrid ta kai zagayen kwata fainal a Copa del Ray
Real Madrid ta kai zagayen kwata fainal a Copa del Ray REUTERS/Jon Nazca
Talla

Madrid ta kai zagayen kwata fainal a gasar da jimillar kwallaye ci 6 da 3 bayan a karawa ta farko ta doke Sevilla ci 3 da 0.

Yanzu Real Madrid ta zarce tarihin da Barcelona ta kafa na buga wasanni 39 ba a samu galabarta ba a kakar 2012.

Sai dai kuma a ranar Lahadi Real Madrid za ta sake gwabzawa ne da Sevilla a La liga wasan da ake ganin zai yi zafi ganin Sevilla ke bi wa Real Madrid a saman Tebur da tazarar maki 4 tsakaninsu kodayake Madrid na da kwanten wasa.

Barcelona kuma na matsayi na uku ne tazarar maki guda tsakaninta da Sevilla.

A gobe ne Barcelona za ta karbi bakuncin Las Palmas kafin Sevilla da Madrid su kece raini a ranar lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.