Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Ina son wasu shekaru 10 ina kwallo- Ronaldo

Cristiano Ronaldo zai ci gaba da murza leda a Real Madrid bayan ya sabunta kwangilar shi ta tsawon shekaru 5 a yau Litinin. Wannan na zuwa bayan abokan wasan shi Gareth Bale da Luka Modric da Toni Kroos sun tsawaita kwangilarsu da kungiyar.

Cristiano Ronaldo tare da Shugaban Real Madrid Florentino Perez
Cristiano Ronaldo tare da Shugaban Real Madrid Florentino Perez REUTERS
Talla

Cristiano Ronaldo ya bayyana fatar ci gaba da taka leda daga nan har zuwa shekaru 10 bayan ya sanya hannu kan yarjejeniyar Karin shekaru 5 da Real Madrid.

Hakan na nufin Cristiano na soni ci gaba da buga kwallo har sai ya kai shekaru 36.

Ana dai sa ran sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar za ta ci gaba da kare Ronaldo a matsayinsa dan wasan kwallon kafa da ya fi karbar kudaden albashi.

Ronlado da Messi ne Mujallar Forces ta bayyana a matsayin 'Yan wasan da aka fi biyan albashi a bana a duniya inda suke karbar kimanin dala Miliyan 88.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.