Isa ga babban shafi
Wasanni

Hull City ta kori kocinta

Kungiyar kwallon kafa ta Hull City ta sallami kocinta Mike Phelan bayan ya gaza kai ta ga gaci a gasar Premier ta Ingila.

Mike Phelan
Mike Phelan sportingnews
Talla

Kungiyar dai ita ce ta karshe a teburin gasar da maki 13, in da ta samu maki uku cakal daga wasanni 9 da ta yi.

Tun a ranar 6 ga watan Nuwamban da ya gabata, raban da Hull ta samu nasara kan wata kungiya, in da a wancan lokacin ta doke Southampton da ci 2-1.

Tuni dai Hull City ta fara neman kwararren Koci da zai maye gurbin Phelan mai shekaru 54, wanda ya karbi aikin horarwar bayan Hull ta raba gari da Steve Bruce a wannan kakar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.