Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta ki barin Bournemouth ta doke ta

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya bayyana cewa, ‘yan wasansa sun jajirce don ganin Bournemouth ba ta doke su a fafatawar da suka yi a gasar Premier ta Ingila. 

Kocin Arsenal Arsène Wenger
Kocin Arsenal Arsène Wenger Reuters
Talla

Bournemouth ce dai ta fara zura kwalleye 2 tun gabanin tafiya hutun rabin lokaci, yayin da ta zura ta uku bayan an dawo daga hutun, lamarin da ya sa aka yi zaton da yiwuwar ta doke Arsenal.

To sai dai a cikin mintina 20 gabanin a tashi wasan na jiya, Arsenal ta farke dukkanin kwallayen uku kuma da haka suka yi canjaras 3-3.

Alexis Sanchez ne ya fara farke wa Arsenal kwallon farko a minti na 70, kafin Lucas Perez ya zura tasa a minti na 75, sai kuma Olivier Giroud da ya jefa kwallon karshe a minti na 92.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.