Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea za ta karfafa 'yan wasanta

Kocin Chelsea, Antonio Conte ya bayyana cewa, da yiwuwar ya karfafa ‘yan wasansa a cikin wannan wata na Janairu da ake bude kasuwar cinikayayyar ‘yan wasa.

Kocin Arsenal Antonio Conte
Kocin Arsenal Antonio Conte Reuters/Alessandro Garofalo
Talla

Conte zai yi haka ne da nufin karfafa gwiwar ‘yan wasansa a fafatawar da suke yi na kokarin lashe kofin Premier a bana.

A yau Laraba ne Chelsea mai jan ragamar teburin gasar ta Premier za ta kai wa Tottenham ziyara don neman lashe wasanni 14 a jere.

Matukar dai Chelsea ta samu nasara a wasan na yau, to lallai za ta bai wa Liverpool mai bi mata a teburi tazar maki 8.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.